Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 6:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Wane ne a cikinku, don damuwarsa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 6:27
14 Iomraidhean Croise  

Na sani dukan abin da Allah ya yi zai dawwama, ba abin da za a ƙara, ko a rage. Allah ya yi haka kuwa domin mutane su zama masu tsoronsa.


Kada kuwa ka rantse da kanka, don ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya fari ko baƙi ba.


“Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu a kan rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuwa jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe, rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba?


To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin jeji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi,


Don haka kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci’ ko? ‘Me za mu sha?’ Ko kuwa, ‘Me za mu sa?’


“Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe ta Allah ce. Wahalce-wahalcen yau ma sun isa wahala.”


Amma Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, Marta! Hankalinki a tashe yake, kina kuma damuwa kan abu da yawa.


Sa'ad da suka kai ku gaban majami'u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa,


Sai ya ce wa almajiransa, “Don haka, ina gaya muku, kada ku damu da batun rayuwarku game da abin da za ku ci, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura.


Amma ga shi, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowaccensu yadda ya nufa.


Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.


Ku jibga masa dukan taraddadinku, domin yana kula da ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan