Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 6:2 - Littafi Mai Tsarki

2 “Wato, in za ka yi sadaka, kada ka yi kwakwazo yadda munafukai suke yi a majami'u da kuma kan hanya don dai mutane su yabe su. Gaskiya nake faɗa muku, sun sami iyakar ladarsu ke nan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 6:2
56 Iomraidhean Croise  

Yakan bayar ga matalauta hannu sake, Alherinsa kuwa dawwamamme ne. Zai zama mai iko wanda ake girmamawa.


Mugu yakan ci bashi, yă ƙi biya, Amma mutumin kirki mai alheri ne, Mai bayarwa hannu sake.


Sa'ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.


Kowa gani yake shi mai biyayya ne, mai aminci. Amma ina? Ko ka yi ƙoƙari ka sami amintacce ɗaya daga cikinsu, ba za ka samu ba.


Ka raba abin da yake hannunka ga mutum bakwai ko takwas, gama ba ka san irin masifar da za ta auka wa duniya ba.


Na aiki Assuriya ta faɗa wa al'ummar da ba ta tsoron Allah, da yaƙi, wato jama'ar da ta sa na yi fushi. Na aike su su yi waso su yi sata, su tattake jama'a kamar ƙura a tituna.”


Ku ci abincinku tare da mayunwata, ku kuma shigo da matalauta, marasa mahalli a cikin gidajenku. Idan kuma kun ga wanda yake tsirara, ku sa masa sutura, kada kuma ku ɓoye fuskokinku ga 'yan'uwanku.


Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.


Ubangiji ya ce, “Ki sa ƙaho a bakinki, Kamar gaggafa, haka maƙiyi ya kawo sura a kan ƙasar Ubangiji, Domin mutanena sun ta da alkawarina, Sun kuma keta dokokina.


Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, da ya ce,


Da safe kuma in kun ga sama ta yi ja, ta kuma gama gari, kukan ce, ‘Yau kam, za a yi hadiri.’ Kuna iya gane yanayin sararin sama, amma ba kwa iya gane alamun zamanin nan.


Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai!


Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa.


Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami'u,


yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da munafukai. Nan za a yi kuka da cizon baki.”


Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome.


“In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, wai don mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan.


Amma in kana yin sadaka, kada hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama yake yi,


“In za ku yi addu'a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'u da kan hanya, wai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun sami iyakar ladansu.


Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake idonka tukuna, sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan'uwanka.


da kuma mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki.


Sai ya ce musu, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, munafukai! Yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Al'umman nan a baka kawai suke girmama ni, Amma a zuci nesa suke da ni.


Gara ku tsarkake cikin, sa'an nan kome zai tsarkaka a gare ku.


Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna son mafifitan mazaunai a majami'u, da kuma gaisuwa a kasuwa.


Ku sayar da mallakarku, ku bayar taimako. Ku samar wa kanku jakar kuɗi da ba ta tsufa, wato, dukiya marar yankewa ke nan a Sama, inda ba ɓarawon da zai gabato, ba kuma asun da zai ɓāta,


Munafukai! Kuna iya gane yanayin ƙasa da na sararin sama, amma me ya sa ba ku iya gane alamun zamanin ba?”


Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe, kowannenku ba ya kwance takarkarinsa ko jakinsa a turke, ya kai shi banruwa ran Asabar?


“Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo a cikin manyan riguna, masu so a gaishe su a kasuwa, masu son mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki.


“Amma kaitonku, ku masu arziki domin kun riga kun sami taku ta'aziyya.


Ƙaƙa kuma za ka iya ce wa ɗan'uwanka, ‘Ya ɗan'uwana, bari in cire maka ɗan hakin da yake a idonka,’ alhali kuwa kai kanka ba ka ga gungumen da yake a naka ido ba? Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake a idonka tukuna sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka.”


Har waɗansu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar idi ne, ko kuwa ya ba gajiyayyu wani abu, don Yahuza ne yake riƙe da jakar kuɗinsu.


Ba na karɓar girma wurin mutane.


Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karɓar girma a junanku, girman da yake daga Allah Makaɗaici kuwa, ba kwa nemansa?


Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.


Shi kuwa mutum ne mai ibada, yana tsoron Allah shi da iyalinsa duka, yana ba jama'a sadaka hanu sake, yana kuma addu'a ga Allah a kai a kai.


ya ce, ‘Ya Karniliyas, an amsa addu'arka sadakarka kuma ta zama abar tunawa ga Allah.


Shi kuwa ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, mene ne?” Mala'ikan kuma ya ce masa, “Addu'arka da sadakarka sun kai har a gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.


Sai masu bi suka ɗaura niyya, kowa gwargwadon ƙarfinsa, su aika wa yan'uwan da suke ƙasar Yahudiya gudunmawa.


To, bayan 'yan shekaru sai na je domin in kai gudunmawa ga jama'armu, in kuma yi sadaka.


A Yafa kuwa akwai wata mai bi, mai suna Tabita, wato Dokas ke nan. Matar nan kuwa lazimar aiki nagari ce, da kuma gudunmawa.


mai ƙarfafa zuciya kuwa, wajen ƙarfafawarsa, mai yin gudunmawa kuwa, yă bayar hannu sake, shugaba yă yi shugabancinsa da himma, mai yin aikin tausayi, yă yi shi da fara'a.


Ko da zan sadaukar da duk abin da na mallaka, in kuma ba da jikina a ƙone, in har ba ni da ƙauna, to, ban amfana da kome ba.


Sai dai kuma suna so mu tuna matalauta, wannan kuwa ko dā ma ina da himmar yi ƙwarai.


Kada ɓarawo ya ƙara yin sata, a maimakon haka sai ya motsa jiki yana aikin gaskiya da hannunsa, har da zai sami abin da zai ba matalauta.


Ba mu kuwa taɓa neman girma ga mutane ba, ko a gare ku, ko ga waɗansu, ko da yake da muna so, da mun mori ikon nan namu na manzannin Almasihu.


Sai dai su yi nagarta da bijinta a wajen aiki nagari, su kasance masu hannu sake, suna alheri.


Na yi farin ciki ƙwarai, zuciyata kuma ta ƙarfafa saboda ƙaunar da kake yi, yă kai 'dan'uwana, domin zukatan tsarkaka sun wartsake ta dalilinka.


Kada kuwa ku daina yin alheri da gudunmawa, domin irin waɗannan su ne suke faranta wa Allah rai.


Duk mai wa'azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al'amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!


Sai Saul ya ce, “Na yi zunubi, amma duk da haka ka darajanta ni a gaban shugabannin mutanena, da gaban Isra'ilawa, ka zo, mu tafi tare domin in yi wa Ubangiji Allah sujada.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan