Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 6:19 - Littafi Mai Tsarki

19 “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda ɓarayi kuma suke karyawa su yi sata.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 “Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 6:19
23 Iomraidhean Croise  

Da dare ɓarayi sukan kutsa kai cikin gidaje, Amma da rana sukan ɓuya, su guje wa haske.


“Idan na ce ga zinariya na dogara, ko zinariya tsantsa ita ce jigona,


Bai kuma fi inuwa ba! Duk abin da yake yi banza ne, Yakan tara dukiya, amma bai san wanda zai more ta ba!


Kada ku dogara da aikin kama-karya. Kada ku sa zuciya za ku ci ribar kome ta wurin fashi. In kuwa dukiyarku ta ƙaru, Kada ku dogara gare ta.


In aka iske ɓarawo yana cikin ƙoƙarin shiga ya yi sata, aka buge shi har ya mutu, to, ba za a nemi alhakin jininsa ga kowa ba,


Dukiya ba ta da wani amfani a ranar mutuwa, amma adalci zai hana ka mutuwa.


Yana da kyau, ya kuma fi kyau a sami hikima da ilimi fiye da zinariya da azurfa.


Allah ne yake ba da hikima, da ilimi, da farin ciki ga wanda yake ƙauna. Amma yakan sa matalauci, mai zunubi, ya yi ta wahalar nema ya tara dukiya, domin Allah ya bayar ga wanda yake ƙauna. Wannan ma aikin banza ne, harbin iska ne kawai.


Azurfarsu da zinariyarsu ba za su cece su A ranar hasalar Ubangiji ba, A cikin zafin kishinsa Dukan duniya za ta hallaka. Zai kawo ƙarshen duniya duka nan da nan.


Yesu ya ce masa, “In kana so ka zama kammalalle, sai ka je ka sayar da duk mallakarka, ka bai wa gajiyayyu, ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”


Sai dai ku tara wa kanku dukiya a Sama, inda ba asu da tsatsa da za su ɓata, inda kuma ba ɓarayin da za su karya su yi sata.


Haka, wanda ya tanada wa kansa dukiya yake, ba shi kuwa da wani tanadi a gun Allah.”


Ku sayar da mallakarku, ku bayar taimako. Ku samar wa kanku jakar kuɗi da ba ta tsufa, wato, dukiya marar yankewa ke nan a Sama, inda ba ɓarawon da zai gabato, ba kuma asun da zai ɓāta,


Amma dai ku sani, da maigida zai san lokacin da ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake, ya hana a shiga masa gida.


Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Har yanzu abu guda ne kawai ya rage maka, ka sayar da duk mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”


Yesu kuwa da ya gan shi haka, ya ce, “Kai! Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah!


Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa.


Kada halinku ya zama na son kuɗi. Ku dangana da abin da kuke da shi, gama Allah kansa ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan