Girma, da iko, da daraja, da nasara, da ɗaukaka duk naka ne, ya Ubangiji, gama dukan abin da yake cikin sammai da duniya naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji. Kai ne Maɗaukaki duka.
Yabez ya roƙi Allah na Isra'ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.
“Amin, amin, Ubangiji ya sa ya zama haka, Ubangiji ya sa annabcin da ka yi ya zama gaskiya, Ubangiji ya komo da kayayyakin Haikalinsa da dukan waɗanda aka kai su zaman talala a Babila.
Za a kore ka daga cikin mutane zuwa jeji ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka sani Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.
Bari ruwan nan ya shiga cikinki, ya sa cikinki ya kumbure, cinyarki kuma ta shanye.” Sai matar ta amsa, ta ce, “Amin, amin, Ubangiji ya sa ya zama haka.”
Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan adam ba. Allah mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ƙarfinku ba, amma a game da gwajin sai ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.
Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.
ashe kuwa, Ubangiji ya san yadda zai kuɓutar da masu tsoronsa daga gwaje-gwaje, ya kuma tsare marasa adalci a kan jiran hukunci, har ya zuwa ranar shari'a,
Sai dattawan nan ashirin da huɗu, da rayayyun halittan nan huɗu, suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, shi da yake zaune a kan kursiyin, suna cewa, “Amin. Halleluya!”
Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.
Tun da yake ka kiyaye maganar da na yi maka ta yin jimiri, Ni ma zan kiyaye ka daga sharrin lokacin nan na gwaji, wanda zai auko wa dukan duniya, don a gwada mazaunan duniya.
“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Lawudikiya haka, ‘Ga maganar tabbataccen nan, Amintaccen Mashaidi mai gaskiya, wanda ta wurinsa dukkan halittar Allah ta kasance.
Sai na ji kowace halittar da take a Sama, da ƙasa, da ƙarƙashin ƙasa, da bisa teku, da kuma dukkan abin da yake cikinsu, suna cewa, “Yabo, da girma, da ɗaukaka, da mulki sun tabbata ga wanda yake a zaune a kan kursiyin, da Ɗan Ragon nan, har abada abadin!”