Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 6:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Ka gafarta mana laifofinmu, Kamar yadda mu ma muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ka gafarta mana laifofinmu, kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 6:12
25 Iomraidhean Croise  

Sai ka riƙa jin roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra'ilawa, idan sun yi addu'a, suna fuskantar wurin nan, sa'ad da ka ji kuma, sai ka gafarta musu.


sai ka ji daga Sama, ka gafarta wa jama'ar Isra'ila zunubinsu, sa'an nan ka sāke komar da su zuwa ƙasar da ka ba kakanninsu.


sai ka ji addu'arsa. Ka kasa kunne gare shi, a wurin zamanka a Sama, ka gafarta masa. Kai kaɗai ka san tunanin dukan mutane. Ka yi da kowa bisa ga abin da ya yi,


Ka gafarta dukan zunubansu, da tayarwar da suka yi maka. Ka sa abokan gabansu su ji tausayinsu.


Amma kakan gafarta mana, Domin mu zama masu tsoronka.


Mai farin ciki ne mutumin da aka gafarta masa zunubansa, Mai farin ciki ne kuma wanda aka gafarta masa laifofinsa.


Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi, wanda ba zai kuɓutar da mai mugunta ba, amma saboda laifin iyaye nakan hukunta 'ya'ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu.”


Ubangiji ya ce, “Yanzu fa, bari mu daidaita al'amarinmu. Duk kun yi ja wur da zunubi, amma zan wanke ku, ku yi fari fat kamar auduga. Zai yiwu zunubinku ya sa ku zama ja wur, amma za ku yi fari fat kamar farin ulu.


Ya Ubangiji, ka ji mu. Ya Ubangiji, ka garfarce mu. Ya Ubangiji, ka saurare mu, ka yi wani abu saboda sunanka. Ya Allahna, kada ka yi jinkiri domin da sunanka ake kiran birninka da jama'arka.”


Wannan jinina ne na tabbatar alkawari, wanda za a zubar saboda mutane da yawa, domin gafarar zunubansu.


Sai aka kawo masa wani shanyayye, kwance a gado. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, ka yi farin ciki, an gafarta maka zunubanka.”


Koyaushe kuka tsaya yin addu'a, in akwai wanda kuke jin haushinsa, ku yafe masa, domin Ubanku da yake Sama shi ma yă yafe muku laifofinku.


Ka gafarta mana zunubanmu, gama mu ma muna gafarta wa duk wanda yake yi mana laifi. Kada ka kai mu wurin jaraba.’ ”


Ko kuwa goma sha takwas ɗin nan da hasumiya ta faɗo a kansu, a Siluwam, ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?


“Kada ku ɗora wa kowa laifi, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yi wa kowa mugun zato, ku ma ba za a yi muku ba. Ku yafe, ku ma sai a yafe muku.


Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku sani albarkacin mutumin nan ne ake sanar da ku gafarar zunubanku.


Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah,


Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah ya yafe muku ta wurin Almasihu.


kuna jure wa juna, in kuma wani yana da ƙara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan