Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 5:9 - Littafi Mai Tsarki

9 “Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su 'ya'yan Allah.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su ’ya’yan Allah.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 5:9
31 Iomraidhean Croise  

Sai Dawuda ya fito don ya tarye su, ya ce musu, “Idan da salama kuka zo wurina don ku taimake ni, to, zuciyata za ta zama ɗaya da taku, amma idan kun zo ne don ku bashe ni ga maƙiyana, to, Allah na kakanninmu ya duba ya shara'anta, da yake ba ni da laifi.”


Na daɗe ƙwarai ina zama tare da mutane marasa son salama!


Kuna so ku ji daɗin rai? Kuna son tsawon rai da farin ciki?


domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.


Saboda haka sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na Sama take cikakke.”


Ba shi yiwuwa su sāke mutuwa, don daidai suke da mala'iku, 'ya'yan Allah ne kuwa, da yake 'ya'yan tashin matattu ne.


Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama 'ya'yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye.


Kashegari kuma waɗansu suna faɗa, sai ya nemi shirya su, ya ce, ‘Ku jama'a, ku 'yan'uwa ne fa, don me kuke cutar juna?’


In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.


Duk waɗanda Ruhun Allah yake bishe su, su ne 'ya'yan Allah.


Ruhu da Kansa ma, tare da namu ruhu suna yin shaida, cewa mu 'ya'yan Allah ne.


Ga shi, duk halitta tana marmari, tana ɗokin ganin bayyanar 'ya'yan Allah.


Amma ɗan'uwa yakan kai ƙarar ɗan'uwa, gaban marasa ba da gaskiya kuma?


Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, ku yi zaman salama, Allah mai zartar da ƙauna da salama kuwa zai kasance a tare da ku.


Saboda haka, mu jakadu ne na Almasihu, wato, Allah na neman mutane ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Almasihu, ku sulhuntu da Allah.


Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci,


Don haka, ni ɗan sarƙa saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi zaman da ya cancanci kiran da aka yi muku,


Na gargaɗi Afodiya, na kuma gargaɗi Sintiki, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.


kuna jure wa juna, in kuma wani yana da ƙara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe.


Ku himmantu ga zaman lafiya da kowa, ku kuma zama a tsarkake, in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan