Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.
Ku nemi Ubangiji, Dukanku masu tawali'u na duniya, Ku waɗanda kuke bin umarninsa. Ku nemi adalci da tawali'u. Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.
Alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa, cewa zai zama magājin duniya, ba ta Shari'a aka yi masa ba, amma domin ya ba da gaskiya ne, shi ya sa Allah ya karɓe shi mai adalci ne.
Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na'am da ita a cikin halin tawali'u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.
Sai dai ku girmama Almasihu a zukatanku da hakikancewa, shi Ubangiji ne. Kullum ku zauna a shirye ku ba da amsa ga duk wanda ya tambaye ku dalilin begen nan naku, amma fa da tawali'u da bangirma.