Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 5:45 - Littafi Mai Tsarki

45 domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

45 don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 5:45
10 Iomraidhean Croise  

Akwai wanda zai iya ƙidaya mala'ikun da suke masa hidima? Akwai wurin da hasken Allah bai haskaka ba?


Shi mai alheri ne ga kowa, Yana juyayin dukan abin da ya halitta.


A zuciya ba su cewa, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu Wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari, Na kaka da na bazara, Wanda yake ba mu lokacin girbi.’


“Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su 'ya'yan Allah.


Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama 'ya'yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye.


Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”


Duk da haka kuwa bai taɓa barin kansa, ba shaida ba, domin yana yin alheri, shi da yake yi muku ruwan sama, da damuna mai albarka, yana ƙosar da ku da abinci, yana kuma faranta muku rai.”


Saboda haka sai ku zama masu koyi da Allah, in ku ƙaunatattun 'ya'yansa ne.


don ku zama marasa abin zargi, sahihai, 'ya'yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya,


Duk wanda yake haifaffen Allah, ba yakan aikata zunubi ba, domin irinsa yana a cikinsa a zaune, ba yakan aikata zunubi ba, da yake shi haifaffen Allah ne.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan