43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan'uwanka, ka ƙi magabcinka.’
43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’
Ka ji ƙaina ya Ubangiji, ka maido mini da lafiyata, Zan kuwa sāka wa magabtana!
Kada ya ɗaukar wa kansa fansa a kan wani ko ya yi ta ƙinsa, amma ya ƙaunaci sauran mutane kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ni ne Ubangiji.
Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.”
“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.’
“Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’
“Kada Ba'ammone ko Bamowabe ya shiga taron jama'ar Ubangiji. Har tsara ta goma ta zuriyarsu ba za su shiga taron jama'ar Ubangiji ba.
Har abada kada ku nemar musu zaman lafiya ko wadata.
“Ku tuna da abin da Amalekawa suka yi muku a hanya, lokacin da kuka fito daga Masar.
Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla.
Wannan kuma shi ne umarnin da muka samu daga gare shi, cewa mai ƙaunar Allah, sai ya ƙaunaci ɗan'uwansa kuma.