Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 5:42 - Littafi Mai Tsarki

42 Kowa ya roƙe ka, ka ba shi, mai neman rance a wurinka kuwa, kada ka hana shi.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

42 Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 5:42
26 Iomraidhean Croise  

Mugu yakan ci bashi, yă ƙi biya, Amma mutumin kirki mai alheri ne, Mai bayarwa hannu sake.


Sa'ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.


Duk abin da yake tunani dukan yini, shi ne a kan abin da yake so ya samu. Amma adali ko ta ƙaƙa yakan bayar da hannu sake.


Ka shuka iri da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.


Saboda haka, ya sarki, sai ka karɓi shawarata, ka daina zunubanka, ka yi adalci. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulakantawa, watakila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.”


In kuma wani ya tilasta maka ku yi tafiyar mil guda tare, to, ku yi tafiyar mil biyu ma.


Gara ku tsarkake cikin, sa'an nan kome zai tsarkaka a gare ku.


Har ma “in maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.”


Kada kuwa ku daina yin alheri da gudunmawa, domin irin waɗannan su ne suke faranta wa Allah rai.


Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.


Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan