Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 5:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Amma ni ina gaya muku, kada ma ku rantse sam, ko da sama, domin ita ce kursiyin Allah,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne;

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 5:34
8 Iomraidhean Croise  

Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa, Yana da kursiyinsa a Sama. Yana kallon dukan mutane Yana sane da abin da suke yi.


Ba wani bambanci. Makoma ɗaya ce, ta adali da ta mugu, da ta mutumin kirki da ta marar kirki, da ta tsattsarka da ta marar tsarki, da ta masu yin sujada da ta marasa yi. Mutumin kirki bai fi mai zunubi ba. Wanda ya yi rantsuwa bai fi wanda bai yi ba.


Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.


Ubangiji ya ce, “Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce. Daga nan wane irin gida za ku iya ginawa domina, wane irin wuri ne kuma zan zauna?


“ ‘Allah ya ce, Sama ita ce kursiyina, Ƙasa kuwa matashin ƙafata. Wane wuri kuma za ku gina mini? Ko kuwa wane wuri ne wurin hutuna?


Amma fiye da kome, 'yan'uwana, kada ku rantse sam, ko da sama, ko da ƙasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. Sai dai in kun ce “I”, ya tsaya a kan “I” ɗin kawai, in kuwa kun ce “A'a”, ya tsaya a kan “A'a” ɗin kawai, don kada a hukunta ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan