Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 5:33 - Littafi Mai Tsarki

33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka rantse a kan ƙarya, sai dai ka cika wa'adin da ka ɗaukar wa Ubangiji.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 5:33
15 Iomraidhean Croise  

Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya, Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.


Ku ba Ubangiji Allahnku abin da kuka alkawarta masa, Dukanku sauran al'umma da kuke kusa, ku kawo masa kyautai. Allah yakan sa mutane su ji tsoronsa,


“Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.


Kada ku yi alkawari da sunana idan dai ba ku da niyyar cika shi, wannan zai jawo wa sunana ƙasƙanci. Ni ne Ubangiji Allahnku.


Duba a kan duwatsu, ƙafafun wanda yake kawo albishir, Wanda yake shelar salama! Ya Yahuza, ka yi bikin idodinka, Ka kuma cika wa'adodinka. Gama mugun ba zai sāke zuwa ya yi gāba da kai ba, An datse shi ƙaƙaf.


“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.’


“Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’


“Idan kun yi wa Ubangiji Allahnku wa'adi, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama Ubangiji Allahnku zai neme shi a gare ku, ba kuwa zai zama zunubi a gare ku ba.


Sai ku cika duk abin da kuka faɗa da bakinku, gama da yardarku ne kuka yi wa Ubangiji Allahnku wa'adi wanda kuka alkawarta.


“ ‘Kada ka rantse da sunan Ubangiji Allahnka a kan ƙarya, gama Ubangiji ba zai kuɓutar da wanda yake rantsewa da sunansa a kan ƙarya ba.


Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Shi ne za ku bauta masa, ku rantse da sunansa.


da fasikai, da masu luɗu, da masu sace mutane, da maƙaryata, da masu shaidar zur, da kuma duk sauran abin da ya sāɓa sahihiyar koyarwar nan,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan