Ubangiji ya ce, “Idan mutum ya saki matarsa, Ta kuwa rabu da shi, har ta auri wani, Ya iya ya komo da ita? Ashe, yin haka ba zai ƙazantar da ƙasar ba? Ya Isra'ila, kin yi karuwanci, Abokan sha'anin karuwancinki, suna da yawa. Za ki sāke komowa wurina? Ni, Ubangiji, na faɗa.
“Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na ce ina ƙin kisan aure, ina ƙinsa sa'ad da waninku ya yi wa matarsa haka nan. Domin haka sai ku kula da kanku kada ku keta alkawari, mutum ya zama mai aminci ga matarsa.”