Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 5:3 - Littafi Mai Tsarki

3 “Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu, gama mulkin sama nasu ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 5:3
55 Iomraidhean Croise  

Amma sa'ad da yake wahala, sai ya roƙi jinƙan Ubangiji Allahnsa, ya ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.


Addu'arsa, da yadda Allah ya karɓi roƙonsa, da dukan zunubinsa, da rashin amincinsa, da wuraren da ya gina masujadai, ya kafa Ashtarot da siffofi, kafin ya ƙasƙantar da kansa, suna nan a rubuce a littafin Hozai.


Bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji yadda tsohonsa, Manassa, ya yi ba, amma shi Amon ya yi ta yin zunubi a kai a kai.


da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah, sa'ad da ka ji maganarsa a kan wurin nan da mazaunan wurin, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yayyage tufafinka ka yi kuka a gabana, ni kuma na ji ka.


in jama'ata waɗanda ake kiransu da sunana za su yi tawali'u, su yi addu'a, su nemi fuskata, su juyo su bar mugayen ayyukansu, sa'an nan sai in ji su daga Sama, in gafarta zunubansu, in kuma warkar da ƙasarsu.


Saboda haka na ga ni ba kome ba ne, Na tuba, ina hurwa da ƙura da toka.”


Albarka ta tabbata ga mutumin da Ba ya karɓar shawarar mugaye, Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi, Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah.


Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Mai farin ciki ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, Mai farin ciki ne shi wanda yake jin daɗin yin biyayya da umarnansa.


Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji, Wanda yake zamansa bisa ga umarnansa!


Mai farin ciki ne mutumin da Allah na Yakubu ne yake taimakonsa, Yana kuma dogara ga Ubangiji Allahnsa,


Ku yi mubaya'a da Ɗan, Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu, Gama yakan yi fushi da sauri. Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!


Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai, Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.


Mai farin ciki ne wanda yake kula da matalauta, Ubangiji zai taimake shi sa'ad da yake shan wahala.


Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah, Zuciya mai ladabi da biyayya, Ba za ka ƙi ba, ya Allah.


Masu farin ciki ne waɗanda suka dogara gare ka, Ya Allah Mai Runduna!


Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu tawali'u, da ka zama ɗaya daga cikin masu girmankai, har da za ka sami rabo daga cikin ganimarsu.


Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.


“Yanzu ku matasa, ku kasa kunne gare ni, Ku yi abin da na ce, za ku yi farin ciki.


Duk da haka dai, Ubangiji yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai, domin a kullum yana aikata abin da yake daidai. Ta wurin dogara ga Ubangiji ake samun farin ciki.


Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.


Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.


Ni kaina na halicci dukan kome ka kome! Ina jin daɗin waɗanda suke da tawali'u, da kuma masu tuba, waɗanda suke tsorona suna kuwa biyayya gare ni.


Ya kai mutum, ya riga ya nuna maka abin da yake mai kyau. Abin da Ubangiji yake so gare ka, shi ne Ka yi adalci, ka ƙaunaci aikata alheri, Ka bi Allah da tawali'u.


A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.


Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”


“Albarka tā tabbata ga idanunku domin suna gani, da kuma kunnuwanku domin suna ji.


Yesu kuwa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Sama na irinsu ne.”


Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangidansa ya dawo zai samu yana yin haka.


Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.


yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”


Ina kuma gaya muku, da yawa za su zo daga gabas da yamma su zauna cin abinci tare da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a Mulkin Sama,


Da Yesu ya ga haka, sai ya ji haushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne.


Amma ya ce, “I, amma albarka tā fi tabbata ga waɗanda suke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”


Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”


Kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka, ni ma nake ba ku iko,


ku ci ku sha tare da ni a mulkina, ku kuma zauna a kursiyai, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila.


“Ruhun Ubangiji yana tare da ni, Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara. Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru, In kuma buɗe wa makafi ido, In kuma 'yanta waɗanda suke a danne,


Sai Yesu ya ce masa, “Wato saboda ka gan ni ka ba da gaskiya? Albarka tā tabbata ga waɗanda ba su gani ba, amma kuwa suka ba da gaskiya.”


Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.


Mai arziki kuma yă yi alfarma da ƙasƙancinsa, gama zai shuɗe kamar hudar ciyawa.


Albarka tā tabbata ga mai jimirin gwaji, domin in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari.


Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?


Sai mala'ikan ya ce mini, “Rubuta wannan, ‘Albarka tā tabbata ga waɗanda aka gayyata, zuwa cin abincin bikin Ɗan Ragon nan.’ ” Ya kuma ce mini, “Wannan ita ce Maganar Allah ta gaskiya.”


Albarka tā tabbata ga masu wanke rigunansu, domin su sami izinin ɗiba daga itacen rai, su kuma shiga birnin ta ƙofa.


Tun da ka ce, kai mai arziki ne, cewa ka wadata ba ka bukatar kome, ba ka sani ba kuwa kai ne matsiyacin, abin yi wa kaito, matalauci, makaho, tsirara kuma.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan