Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 5:29 - Littafi Mai Tsarki

29 In idonka na dama yana sa ka yi laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa duk jikinka ɗungum a Gidan Wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 5:29
22 Iomraidhean Croise  

Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta.


Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”


Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?


Duk da haka, don kada mu ba su haushi, ka je teku ka yi fatsa, kifin da ka fara kamawa kuwa shi za ka ɗauka. In ka buɗe bakinsa za ka sami shekel guda a ciki. To, sai ka ɗauki shekel ɗin nan ka kai musu, wato, nawa da naka.”


Akwai waɗanda aka haifa babanni, akwai waɗanda mutane ne suka mai da su babanni. Akwai kuma waɗanda suka mai da kansu babanni domin ƙaunar Mulkin Sama. Duk mai iya ɗaukar maganar nan, yă ɗauka.”


Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan kewaye ƙasashe da tekuna don samun almajiri ɗaya tak, in kuwa kun samu, kukan mai da shi ɗan wuta fiye da ku, ninkin ba ninkin.


Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta?


Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.


In kuma hannunka na dama, yana sa ka yi laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa jikinka ɗungum a Gidan Wuta.”


Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa?


Amma zan gaya muku wanda za ku tsorata. Ku ji tsoron wannan da in ya kashe, yana da ikon jefawa a cikin Gidan Wuta. Hakika, ina gaya muku, shi za ku ji tsoro!


Wato, mun sani an gicciye halayenmu na dā tare da shi, domin a hallakar da ikon nan namu mai zunnubi, kada mu ƙara bauta wa zunubi.


In kuna zaman halin mutuntaka, za ku mutu ke nan, amma in da ikon Ruhu kuka kashe ayyukan nan na halin mutuntaka, sai ku rayu.


Amma ina azabta jikina ne, don in bautar da shi, kada bayan da na yi wa waɗansu wa'azi, ni da kaina a yar da ni.


Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha'awace-sha'awace iri iri.


Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha'awace-sha'wacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha'awa, da mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan