Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 5:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Ka hanzarta shiryawa da mai ƙararka tun kuna tafiya gaban shari'a, don kada mai kararka ya bashe ka ga alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga dogari, a kuma jefa ka a kurkuku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 “Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 5:25
19 Iomraidhean Croise  

“Yanzu fa, Ayuba, sai ka yi sulhu da Allah, Ka daina ɗaukarsa kamar maƙiyinka, In ka yi haka, to, za ka sami albarka.


Saboda haka dukan jama'arka masu biyayya, Za su yi addu'a gare ka, lokacin bukata. Sa'ad da babbar rigyawa ta malalo, Ba za ta kai wurinsu ba.


Kada ka yi garajen kai ƙara a majalisa. Idan wani mashaidi ya nuna kai kake da kuskure, me za ka yi?


Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin gidan babban firist. Da ya shiga, sai ya zauna tare da dogaran Haikali, don ya ga ƙarshen abin.


A garin nan kuwa da wata wadda mijinta ya mutu, sai ta riƙa zuwa wurinsa, tana ce masa, ‘Ka shiga tsakanina da abokin gābana.’


Domin ya ce, “Na saurare ka a lokacin samun karɓuwa, Na kuma taimake ka a ranar ceto.” Ga shi, yanzu ne lokacin samun karɓuwa! Ga shi kuma, yau ce ranar ceto!


Kun dai sani daga baya, da ya so yă gāji albarkar nan, sai aka ƙi shi, domin bai sami hanyar tuba ba, ko da yake ya yi ta nemanta har da hawaye.


Sai dai kowace rana ku ƙarfafa wa juna zuciya muddin akwai “Yau”, don kada kowannenku ya taurare, ta yaudarar zunubi.


Saboda haka, kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau in kun ji muryarsa,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan