Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 5:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Saboda haka, in kana cikin miƙa sadakarka a kan bagadin hadaya, a nan kuma ka tuna ɗan'uwanka na da wata magana game da kai,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 5:23
17 Iomraidhean Croise  

Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir'auna, “Yau, na tuna da laifofina.


Sarki kuma ya ce masa, “Ka sani sarai irin duk muguntar da ka yi wa tsohona, Dawuda. Haka kuma Ubangiji zai sāka maka bisa ga muguntarka.


Kullum raina yana tunanin azabaina, Raina kuwa ya karai.


domin ki tuna, ki gigice, ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, sa'ad da na gafarta miki dukan abin da kika aikata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”


Gama ƙauna nake so, ba sadaka ba, Sanin Allah kuma fiye da hadayu na ƙonawa.


Ku makafi! Wanne ya fi girma, sadakar ko kuwa bagaden hadaya da yake tsarkake sadakar?


sai ka dakatar da sadakarka a gaban bagadin hadaya tukuna, ka je ku shirya da ɗan'uwanka, sa'an nan ka zo ka miƙa sadakarka.


Sai Yesu ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”


Koyaushe kuka tsaya yin addu'a, in akwai wanda kuke jin haushinsa, ku yafe masa, domin Ubanku da yake Sama shi ma yă yafe muku laifofinku.


Sai Zakka ya miƙe, ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ka ga, rabin mallakata zan ba gajiyayyu. Kowa na zalunta kuwa, zan mayar masa da ninki huɗu.”


Sai Sama'ila ya ce, “Me Ubangiji ya fi so? Biyayya, ko kuwa sadakoki da hadayu? Ya fi kyau a yi masa biyayya, da a miƙa masa hadayar tumaki mafi kyau.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan