Mattiyu 5:19 - Littafi Mai Tsarki19 Don haka duk wanda ya yar da umarni ɗaya mafi ƙanƙanta daga cikin umarnan nan, har ya koya wa mutane haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a Mulkin Sama. Duk wanda ya bi su kuwa, har ya koyar da su, za a ce da shi mai girma a Mulkin Sama. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202019 Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama. Faic an caibideil |