Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 5:17 - Littafi Mai Tsarki

17 “Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zo ne ba domin in shafe su ba, sai dai domin in cika su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 “Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 5:17
16 Iomraidhean Croise  

Ubangiji shi Allah ne da ya ƙosa ya yi ceto saboda gaskiyarsa, Saboda haka yana so a girmama koyarwarsa,


Amma Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin haka ne ya dace mu cika dukan adalci.” Sa'an nan Yahaya ya yardar masa.


Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”


Duk da haka, zai fi sauƙi sararin sama da ƙasa su shuɗe, da ɗigo ɗaya na Attaura ya gushe.”


To, a Attaura Musa ya umarce mu mu kashe irin waɗannan da jifa, kai kuwa me ka ce?”


suka ce, “Mutumin nan na rarrashin mutane, wai su bauta wa Allah ta hanyar da Shari'ar ta hana.”


suna ihu suna cewa, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku taimaka! Ga mutumin da yake bi ko'ina yana koya wa mutane su raina jama'armu da Shari'a, da kuma wannan wuri. Banda haka kuma har ma ya kawo al'ummai a cikin Haikalin, ya ƙazantar da wurin nan tsattsarka.”


Sai suka gabatar da masu shaidar zur, suka ce, “Mutumin nan ba ya rabuwa da kushe tsattsarkan wurin nan, da kuma Attaura,


Domin Almasihu shi ne cikamakin Shari'a, domin kowane mai ba da gaskiya yă sami adalcin Allah.


Wato mun soke Shari'a ke nan ta bangaskiyar nan? A'a, ko kusa! Sai tabbatar da ita muka yi.


Wannan kuwa domin a cika hakkokin Shari'a ne a gare mu, mu da ba zaman halin mutuntaka muke yi ba, sai dai na Ruhu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan