don ku zama marasa abin zargi, sahihai, 'ya'yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya,
Asirtacciyar ma'anar taurarin nan bakwai da ka gani a hannuna na dama kuwa, da kuma fitilun nan bakwai na zinariya, to, su taurarin nan bakwai, mala'iku ne na ikilisiyoyin nan bakwai, fitilun nan bakwai kuwa, ikkilisiya bakwai ɗin ne.
Ka tuna da komawa bayan da ka yi fa, ka tuba, ka yi irin aikin da ka yi tun daga farko. In ba haka ba, zan zo a gare ka in kawar da fitilarka daga wurin zamanta, sai ko in ka tuba.