Za a kuma kore ka daga cikin mutane zuwa jeji, ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.”
Su ne marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantar da hankalinsu, don kada hasken bisharar ɗaukakar Almasihu, shi da yake surar Allah, ya haskaka su.
Sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada, amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka, waɗanda suke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Domin gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.