Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 4:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Har wa yau dai, sai Iblis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo ƙwarai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 4:8
13 Iomraidhean Croise  

Sai ya nuna wadatar mulkinsa, da martabarsa, da darajarsa har kwanaki masu yawa, wato kwana ɗari da tamanin.


Ya faɗa musu darajar wadatarsa, da yawan 'ya'yansa, da yawan matsayin da sarki ya girmama shi da su, da yadda sarki ya ciyar da shi gaba fiye da sarakuna da barorin sarki.


sai ya ce, “Ashe, wannan ba ita ce Babila babba wadda ni da kaina na gina, da ƙarfin ikona don ta zama fādar sarauta, don darajar ɗaukakata?”


Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Tsaya kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa zan tafi can, in ga ko Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Ya kuwa tafi wani faƙo a kan tudu.


Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?


Sa'an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali,


Domin Uban na ƙaunar Ɗan, yana kuma nuna masa duk abin da shi kansa yake yi, har ma zai nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan, domin ku yi al'ajabi.


Domin “Duk ɗan adam kamar ciyawa yake, Duk darajarsa kamar furen ciyawa take, Ciyawar takan bushe, furen yakan kaɗe,


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan