Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 4:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Sai Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 4:7
21 Iomraidhean Croise  

Suka cika da sha'awa cikin hamada, Suka jarraba Allah,


Da gangan suka jarraba Allah, Da suka ce ya ba su irin abincin da suke so.


Suka yi ta jarraba Allah a kai a kai, Suka kuwa sa Mai Tsarki na Isra'ila yin fushi.


Amma sai suka yi wa Allah Mai Iko Dukka tawaye, Suka jarraba shi. Ba su kiyaye dokokinsa ba,


A can suka gwada ni suka jarraba ni, Ko da yake da idanunsu suka ga abin da na yi dominsu.


Domin haka jama'a suka zargi Musa suka ce, “Ba mu ruwa, mu sha.” Musa ya amsa musu ya ce, “Don me kuke zargina? Don me kuke gwada Ubangiji?”


Sai aka sa wa wurin suna, “Masaha” da “Meriba”, saboda Isra'ilawa suka yi husuma, suka kuma jarraba Ubangiji suna cewa, “Ubangiji yana tare da mu, ko babu?”


Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga 'yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”


A ganinmu masu girmankai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suke yi ba, amma sukan jarraba Allah da mugayen ayyukansu su kuwa zauna lafiya.’ ”


dukan mutanen da suka ga ɗaukakata da alamuna waɗanda na aikata a Masar, da kuma a jejin, suka kuwa jarraba ni har sau goma, ba su kuma yi biyayya da maganata ba,


Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa, “ ‘Kai ne ka shiryar da 'yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”


Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini. Wannan aikin Ubangiji ne, A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’


Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa, ‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”


Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, “ ‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba, Sai dai da kowace maganar da yake fitowa daga wurin Allah.’ ”


Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai kuwa an ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”


Saboda haka, don me kuke gwada Allah, ta ɗora wa almajiran nan kayan da mu, duk da kakanninmu, muka kasa ɗauka?


Amma Bitrus ya ce mata, “Ƙaƙa kuka gama baki ku gwada Ruhun Ubangiji? Kin ji tafiyar waɗanda suka binne mijinki, har sun iso bakin ƙofa ma, za su kuwa ɗauke ki, su fitar da ke.”


Kada kuma mu gwada Ubangiji yadda waɗansu suka yi, har macizai suka hallaka su.


“Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Masaha.


A inda kakanninku suka gwada ni, suka jarraba ni, Suna ganin ayyukana har shekara arba'in.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan