Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 4:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sa'an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 4:5
11 Iomraidhean Croise  

Tsawon shirayi daga gaban Haikalin ya yi daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, sa'an nan tsayinsa kamu ɗari da ashirin. Aka shafe ciki da zinariya tsantsa.


Shugabannin jama'a kuwa suka zauna a Urushalima. Sauran jama'a kuma suka jefa kuri'a don a sami mutum guda daga cikin goma wanda zai zauna a Urushalima, wato tsattsarkan birni, sauran tara kuwa su yi zamansu a sauran garuruwa.


Dukan Lawiyawa da suke a tsattsarkan birni su ɗari biyu da tamanin da huɗu ne.


Amma duk da haka kuna fāriya, da cewa Ku ne mazaunan birni mai tsarki, Kuna kuma dogara ga Allah na Isra'ila, Wanda sunansa Ubangiji, Mai Runduna.


Urushalima, ki ƙarfafa, ki yi girma kuma! Birni mai tsarki na Allah, Ki yafa wa kanki jamali! Arna ba za su ƙara shiga ta ƙofofinki ba.


Ya Ubangiji, saboda dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hasalarka da ka yi da birninka Urushalima, tsattsarkan tudunka. Gama saboda zunubanmu da muguntar kakanninmu, Urushalima da jama'arka sun zama abin ba'a ga waɗanda suke kewaye da mu.


“An ƙayyade wa jama'arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa'in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa'an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake Haikali.


Suka firfito daga kaburburan, bayan ya tashi daga matattu, sai suka shiga tsattsarkan birnin, suka bayyana ga mutane da yawa.


Sai kuma ya kai shi Urushalima, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa daga nan,


Yesu ya amsa masa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina in ba an ba ka daga Sama ba, saboda haka wanda ya bāshe ni gare ka ya fi ka zunubi.”


amma kada ka auna harabar Haikalin, ka ƙyale ta, domin an ba da ita ga al'ummai, za su tattake tsattsarkan birnin nan har wata arba'in da biyu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan