Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 4:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Taro masu yawan gaske suka bi shi daga ƙasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da ƙasar Yahudiya, har ma daga hayin Kogin Urdun.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Taron mutane mai yawa daga Galili, Dekafolis, Urushalima, Yahudiya da kuma yankin hayin Urdun suka bi shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 4:25
11 Iomraidhean Croise  

Da Yesu ya gane haka, ya tashi daga nan. Sai jama'a da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su duka.


Taro mai yawan gaske suka bi shi, ya kuwa warkar da su a can.


“Ƙasar Zabaluna da ƙasar Naftali, Da bakin bahar, da hayin Kogin Urdun, Da kuma ƙasar Galili ta al'ummai,


Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Da ya zauna, almajiransa kuma suka zo gunsa.


Da ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawan gaske suka bi shi.


Sai ya tafi, ya shiga baza labari a Dikafolis na irin manyan abubuwan da Yesu ya yi masa. Duk mutane kuwa suka yi al'ajabi.


Da Asabar ta yi, sai ya fara koyarwa a majami'a. Mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki, suna cewa, “Ina mutumin nan ya sami wannan abu duka? Wace hikima ce aka ba shi haka? Dubi irin waɗannan mu'ujizan da ake aikatawa ta hannunsa!


Sai ya komo daga wajen Taya, ya bi ta Sidon ya je Tekun Galili ta Dikafolis.


Sai ya gangaro tare da su, ya tsaya a wani sarari. Ga kuwa babban taro masu binsa, da kuma taro masu yawan gaske daga duk ƙasar Yahudiya da Urushalima, da kuma yankin ƙasar Taya da Sidon da yake bakin bahar, waɗanda suka zo su saurare shi, a kuma warkar da cuce-cucensu.


Duk taron suka nema su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan