Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 4:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 4:24
41 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Suriya ta Dimashƙu. Suriyawa suka zama talakawan Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Duk inda Dawuda ya tafi, Ubangiji yakan taimake shi.


Sarauniyar Sheba ta ji labarin sunan da Sulemanu ya yi ta dalilin sunan Ubangiji, ta zo don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya.


Gama ya fi dukan mutane hikima, ya fi Etan Ba'ezrahe, da Heman, da Kalkol, da Darda, 'ya'yan Mahol. Ya shahara a ƙasashen da suke kewaye da shi.


Sunan Dawuda kuma ya kai ko'ina cikin dukan ƙasashe. Ubangiji kuwa ya sa dukan al'ummai su ji tsoron Dawuda.


A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda Haikalin Allahna, wato zinariya saboda kayayyakin zinariya, azurfa saboda kayayyakin azurfa, tagulla saboda kayayyakin tagulla, baƙin ƙarfe saboda kayayyakin baƙin ƙarfe, itace kuwa saboda kayayyakin itace, da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri iri.


Ya ce, “In za ku himmantu ku yi biyayya da ni, ni da nake Ubangiji Allahnku, sai ku aikata abin da yake daidai a gare ni, ku kuma kiyaye umarnaina da dokokina duka, to, ba zan sa muku cuce-cuce irin waɗanda na sa wa Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”


Sai aka kawo masa wani beben makaho mai aljan, ya kuwa warkar da shi, har beben ya yi magana, ya kuma gani.


A lokacin nan sarki Hirudus ya ji labarin shaharar Yesu.


Ga wata Bakan'aniya mutuniyar ƙasar, ta zo, ta ɗaga murya ta ce, “Ya Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina. Wani aljani ya bugi 'yata, ba yadda take.”


“Ya Ubangiji, ka ji tausayin ɗana, yana farfaɗiya, yana shan wuya ƙwarai, sau da yawa yakan faɗa wuta da kuma ruwa.


Sai Yesu ya tsawata masa, aljanin kuma ya rabu da shi. Nan take yaron ya warke.


Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.


Da ya isa wancan hayi a ƙasar Garasinawa, mutum biyu masu aljannu suka fito daga makabarta suka tarye shi. Don kuwa su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bi ta wannan hanya.


Masu kiwon aladen suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin kome da kome, da kuma abin da ya auku ga masu aljannun.


ya ce, “Ya Ubangiji, yarona na kwance a gida, ya zama shanyayye, yana shan azaba ƙwarai.”


Wannan labarin kuwa ya bazu a duk ƙasar.


Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.


Nan da nan sai ya shahara a ko'ina duk kewayen ƙasar Galili.


Da magariba, bayan faɗuwar rana, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya, da masu aljannu.


Sai suka kawo masa wani shanyayye, mutum huɗu suna ɗauke da shi.


Da suka kāsa kusatarsa don yawan mutane, suka buɗe rufin soron ta sama da shi. Da suka huda ƙofa kuwa, suka zura gadon da shanyayye yake kwance a kai.


Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta maka zunubanka’, ko kuwa a ce, ‘Tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka yi tafiya’?


Wannan shi ne ƙirga na fari da aka yi a zamanin Kiriniyas, mai mulkin ƙasar Suriya.


Yesu ya koma ƙasar Galili, ikon Ruhu yana tare da shi. Labarinsa ya bazu a dukan kewayen.


Sai ya tashi daga majami'a, ya shiga gidan Bitrus. Surukar Bitrus kuwa tana fama da mugun zazzaɓi, sai suka roƙe shi saboda ita.


Amma duk da haka labarinsa sai ƙara yaɗuwa yake yi, har taro masu yawan gaske suka yi ta zuwa domin su saurare shi, a kuma warkar da su daga rashin lafiyarsu.


Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya”, sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka tafi gida.”


Wannan labarin nasa kuwa ya bazu a dukan ƙasar Yahudiya da kewayenta.


Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, wannan magana, ai, ba ta mai iska ba ce. Ashe, iska tana iya buɗe wa makaho ido?”


wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.


da wannan takarda cewa, “Daga 'yan'uwanku, manzanni da dattawan Ikkilisiya, zuwa ga 'yan'uwanmu na al'ummai a Antakiya da ƙasar Suriya da ta Kilikiya. Gaisuwa mai yawa.


Bulus ya zazzaga ƙasar Suriya da ta Kilikiya, yana ta ƙarfafa Ikilisiyoyi.


Da aka yi haka sai duk sauran marasa lafiya a tsibirin suka riƙa zuwa ana warkar da su.


Domin da yawa masu baƙaƙen aljannu suka rabu da su, aljannun kuwa na ta ihu. Shanyayyu da guragu da yawa kuma an warkar da su.


Ubangiji yana tare da Joshuwa, ya kuwa yi suna cikin dukan ƙasar.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan