Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 4:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 4:23
46 Iomraidhean Croise  

Ya gafarta dukan zunubaina, Ya kuma warkar da dukan cuce-cucena.


Sun yi niyya su murƙushe mu sarai, Sun ƙone kowane tsattsarkan wuri na ƙasar.


Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, ana tsarkake kutare, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.


Sai ya ci gaba daga nan ya shiga majami'arsu.


Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.


Da ya zo garinsu, ya koya musu a majami'arsu, har suka yi mamaki, suka ce, “Daga ina mutumin nan ya sami wannan hikima haka, da kuma mu'ujizan nan?


Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.


Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko'ina a duniya domin shaida ga dukkan al'ummai. Sa'an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”


yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”


Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.


To, bayan an tsare Yahaya, sai Yesu ya shigo ƙasar Galili, yana yin bisharar Allah,


Suka shiga Kafarnahum. Ran Asabar kuwa, ya shiga majami'a yana koyarwa.


Ya gama ƙasar Galili duk yana wa'azi a majami'unsu, yana kuma fitar wa mutane aljannu.


saboda ya riga ya warkar da mutane da yawa, har ya kai ga duk masu cuta na dannowa wurinsa domin su taɓa shi.


Da Asabar ta yi, sai ya fara koyarwa a majami'a. Mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki, suna cewa, “Ina mutumin nan ya sami wannan abu duka? Wace hikima ce aka ba shi haka? Dubi irin waɗannan mu'ujizan da ake aikatawa ta hannunsa!


Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu. Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.


Ku warkar da marasa lafiya da suke cikinsa, ku kuma ce musu, ‘Mulkin Allah ya kusato ku.’


Wata rana yana koyarwa a wata majami'a ran Asabar,


“Attaura da litattafan annabawa suna nan har ya zuwa ga Yahaya, daga lokacin nan kuwa ake yin bisharar Mulkin Allah, kowa kuma yana kutsawa zuwa ciki.


Wata rana yana koyar da mutane a Haikali, yana yi musu bishara, sai ga manyan firistoci da malaman Attaura, da shugabanni suka matso,


Yesu ya koma ƙasar Galili, ikon Ruhu yana tare da shi. Labarinsa ya bazu a dukan kewayen.


Wata rana na koyarwa, waɗansu Farisiyawa kuwa da masanan Attaura da suka fito daga kowane gari na ƙasar Galili, da na ƙasar Yahudiya, daga kuma Urushalima, suna nan a zaune. Ikon Ubangiji na warkarwa kuwa yana nan.


Sai ya gangaro tare da su, ya tsaya a wani sarari. Ga kuwa babban taro masu binsa, da kuma taro masu yawan gaske daga duk ƙasar Yahudiya da Urushalima, da kuma yankin ƙasar Taya da Sidon da yake bakin bahar, waɗanda suka zo su saurare shi, a kuma warkar da cuce-cucensu.


A wata Asabar kuma ya shiga majami'a, yana koyarwa. Akwai kuwa wani mutum a ciki wanda hannunsa na dama ya shanye.


Nan take Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani.


Sai ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.


Ba da daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa'azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi,


Ganin haka sai taro masu yawa suka bi shi. Ya kuwa yi musu maraba, ya yi musu maganar Mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkewa.


Sai Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu. Amma kai kuwa, tafi ka sanar da Mulkin Allah.”


Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba.


Wannan kuwa a majami'a ya faɗa, sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum.


Bayan haka, Yesu ya riƙa zagawa a Ƙasar Galili, bai yarda ya zaga ta Yahudiya ba, don Yahudawa suna neman kashe shi.


wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.


Ya kuma yi ta yin muhawwara a majami'a a kowace Asabar, yana ta rinjayar Yahudawa da al'ummai.


To, ga shi, yanzu na san dukanku ba za ku ƙara ganina ba, ku da na zazzaga cikinku ina yi muku bisharar Mulkin Allah.


yana ta wa'azin Mulkin Allah, da koyar da al'amarin Ubangiji Yesu Almasihu gabagaɗi, ba tare da wani hani ba.


Ta ƙaƙa kuma za su yi wa'azi, in ba aikarsu aka yi ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaya zai kasance a isowar masu kawo bishara!”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan