Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 4:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Da ya ci gaba sai ya ga waɗansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da ubansu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 4:21
12 Iomraidhean Croise  

To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya,


Bayan kwana shida sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da ɗan'uwansa Yahaya, ya kai su a kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai.


Sai ya ɗauki Bitrus da 'ya'yan nan na Zabadi biyu, ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.


Nan da nan, sai suka watsar da tarunansu, suka bi shi.


Nan take suka bar jirgin duk da ubansu, suka bi shi.


da Yakubu ɗan Zabadi, da kuma ɗan'uwansa Yahaya, ya sa musu suna Buwanarjis, wato 'ya'yan tsawa.


Bai bar kowa ya bi shi ba sai Bitrus, da Yakubu, da kuma Yahaya ɗan'uwan Yakubu.


Bitrus, da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai, da Nata'ala na Kana ta ƙasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma waɗansu almajiransa biyu, duk suna nan tare,


har ma ya sare Yakubu ɗan'uwan Yahaya da takobi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan