Elisha kuwa ya koma, ya kama shanun noman, ya yanka, ya dafa su da karkiyoyinsu. Ya raba wa mutane, suka ci. Sa'an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya zama mai taimakonsa.
Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.
Da ya ci gaba sai ya ga waɗansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da ubansu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su.