Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 4:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Mazaunan duhu sun ga babban haske, Mazaunan bakin mutuwa da fargabarta, Haske ya keto musu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 mutanen da suke zama cikin duhu sun ga babban haske; haske kuma ya haskaka a kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 4:16
14 Iomraidhean Croise  

Ƙasa mai duhu, da inuwoyi da ɗimuwa Inda ko haske ma kansa duhu ne.”


Ka sa ta zama ranar duhu baƙi ƙirin. Ka rufe ta da gizagizai, kada hasken rana ya haskaka ta.


Ba wani duhu, ko duhu baƙi ƙirin Inda masu aikata mugunta za su ɓuya.


Duk da haka ka ƙi taimakonmu da namomin jejin nan, Ka bar mu a cikin duhu baƙi ƙirin.


Ba sauran baƙin ciki ga wadda take shan azaba. Dā an ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zabaluna da na Naftali, amma nan gaba wannan jiha za ta sami daraja, tun daga Bahar Maliya, zuwa gabashin ƙasar a wancan sashe na Urdun, har zuwa Galili kanta, wurin da baƙi suke zaune.


Jama'ar da suka yi tafiya cikin duhu, Sun ga babban haske! Suka zauna a inuwar mutuwa, Amma yanzu haske ya haskaka su.


Ku girmama Ubangiji Allahnku, Kafin ya kawo duhu, Kafin kuma ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan dutse, da duhu duhu, Sa'ad da kuke neman haske, sai ya maishe shi duhu, Ya maishe shi duhu baƙi ƙirin.


Ubangiji ne ya yi taurarin Kaza da 'ya'yanta Da mai farauta da kare. Ya mai da duhu haske, Rana kuwa dare. Shi ya kirawo ruwan teku ya bayyana, Ya shimfiɗa shi a bisa ƙasa. Sunansa Ubangiji ne.


Ya maƙiyina, kada ka yi murna a kaina, Gama sa'ad da na fāɗi, zan tashi kuma. Sa'ad da na zauna cikin duhu, Ubangiji zai haskaka ni.


Haske mai bayyana wa alummai hanyarka, Da kuma ɗaukakar jama'arka Isra'ila.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan