Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 4:15 - Littafi Mai Tsarki

15 “Ƙasar Zabaluna da ƙasar Naftali, Da bakin bahar, da hayin Kogin Urdun, Da kuma ƙasar Galili ta al'ummai,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 “Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali, da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun, wannan yankin Galili ta Al’ummai,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 4:15
9 Iomraidhean Croise  

Hiram, Sarkin Taya, kuwa ya ba Sulemanu katakan itacen al'ul da na fir da zinariya, iyakar yadda yake bukata. Sarki Sulemanu kuwa ya ba Hiram garuruwa ashirin a jihar Galili.


A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.


Ba sauran baƙin ciki ga wadda take shan azaba. Dā an ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zabaluna da na Naftali, amma nan gaba wannan jiha za ta sami daraja, tun daga Bahar Maliya, zuwa gabashin ƙasar a wancan sashe na Urdun, har zuwa Galili kanta, wurin da baƙi suke zaune.


Ya kuma bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin teku, a kan iyakar ƙasar Zabaluna da Naftali,


domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,


Taro masu yawan gaske suka bi shi daga ƙasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da ƙasar Yahudiya, har ma daga hayin Kogin Urdun.


Sai ya fara ta kan littattafan Musa da na dukan annabawa, ya yi ta bayyana musu abubuwan da suka shafe shi a dukan Littattafai.


Saboda haka suka keɓe Kedesh ta Galili a ƙasar tuddai ta Naftali, da Shekem ta ƙasar tuddai ta Ifraimu, da Kiriyat-arba, wato Hebron, ta ƙasar tuddai ta Yahuza.


Daga cikin rabon kabilar Naftali aka ba su birane uku, su ne, Kedesh ta Galili da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Hammon da wuraren kiwo nata, da Kartan da wuraren kiwo nata.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan