14 domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,
14 don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,
An yi wannan ne duk, don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa,
ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya faɗa ne ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kirawo Ɗana.”
Sai ya je ya zauna a wani gari wai shi Nazarat, domin a cika faɗar annabawa cewa, “Za a kira shi Banazare.”
To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai a kan lalle wannan abu ya kasance?”
Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.
Ya kuma bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin teku, a kan iyakar ƙasar Zabaluna da Naftali,
“Ƙasar Zabaluna da ƙasar Naftali, Da bakin bahar, da hayin Kogin Urdun, Da kuma ƙasar Galili ta al'ummai,
Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa, “Da kansa ya ɗebe rashin lafiyarmu, ya ɗauke cucecucenmu.”
Ina dai gaya muku, lalle ne a cika wannan Nassi a kaina cewa, ‘An lasafta shi a cikin masu laifi.’ Gama abin da aka faɗa a kaina, tabbatarsa ta zo.”
Ya kuma ce musu, “Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare, cewa lalle ne a cika duk abin da yake rubuce game da ni a Attaura ta Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.”
An yi wannan kuwa domin a cika maganar da yake a rubuce a cikin Shari'arsu cewa, “Sun ƙi ni ba dalili.”
Bayan haka, Yesu da ya san duk an gama kome, domin a cika Nassi sai ya ce, “Ina jin ƙishirwa.”