Rabuwata da kai ke da wuya, sai Ruhun Ubangiji ya kai ka wurin da ban sani ba, don haka, in na tafi na faɗa wa Ahab, in bai same ka ba, to, ni zai kashe, ko da yake ni baranka, tun ina saurayi nake tsoron Ubangiji.
suka kuma ce masa, “Yanzu fa, ga mu mu hamsin ƙarfafa. Bari mu tafi mu nemo maigidanka, mai yiwuwa ne Ruhun Ubangiji ya ɗauke shi, ya jefa shi kan wani dutse, ko cikin wani kwari.” Elisha ya ce, “Kada ku tafi.”
Sai Ruhu ya ɗaga ni sama, ya kai ni ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji wadda dake fuskantar gabas. Sai ga mutum ashirin da biyar a bakin ƙofar. A cikinsu na ga Yazaniya ɗan Azzur, da Felatiya ɗan Benaiya, shugabannin jama'a.
Sai ya miƙa hannu, ya kama zankon kaina. Ruhu kuma ya ɗaga ni bisa tsakanin sama da ƙasa, ya kai ni Urushalima cikin wahayi zuwa ƙofar farfajiya ta ciki, wadda take fuskantar arewa, inda mazaunin siffa ta tsokano kishi yake.