Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 3:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Kada kuwa ku ɗauka a ranku cewa, Ibrahim ne ubanku, domin ina gaya muku, Allah yana da ikon ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya da duwatsun nan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 3:9
22 Iomraidhean Croise  

“Ɗan mutum, mazaunan wuraren nan da aka lalatar a ƙasar Isra'ila, suna cewa, ‘Ibrahim shi kaɗai ne, duk da haka an ba shi ƙasar duka, balle fa mu da muke da yawa, lalle ƙasar tamu ce.’


Don daga ciki ne, wato daga zuciyar mutum, mugayen tunani yake fitowa, kamar su fasikanci, da sata, da kisankai, da zina,


Sai ya ce a ransa, ‘To, ƙaƙa zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’


Sai ya yi kira ya ce, ‘Baba Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiko Li'azaru ya tsoma kan yatsarsa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.’


Ya amsa ya ce, “Ina dai gaya muku, ko waɗannan sun yi shiru, to, duwatsu ma sai su ɗauki sowa.”


Ku yi aikin da zai nuna tubanku, kada ma ku ko fara cewa a ranku Ibrahim ne ubanku. Ina dai gaya muku Allah yana da iko ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya daga duwatsun nan.


Da Yesu ya gane wuswasinsu, ya amsa musu ya ce, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku?


To, da Bafarisiyen da ya kira shi ya ga haka, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce, da kuma ko wace irin mace ce wannan da yake taɓa shi, don mai zunubi ce.”


Suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne, ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya kuma za ka ce za a 'yanta mu?”


Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuwa kuna neman kashe ni, don maganata ba ta shigarku.


Wato ka fi ubanmu Ibrahim ne, ya kuwa mutu? Annabawa ma sun mutu! Wa ka mai da kanka ne?”


“Ya ku 'yan'uwa, zuriyar Ibrahim, da kuma sauran masu tsoron Allah a cikinku, mu fa aka aiko wa kalmar ceton nan.


Bitrus ya ba da labari yadda Allah ya fara kula da al'ummai, domin ya keɓe wata jama'a daga cikinsu ta zama tasa.


To, me ke nan za mu ce a game da Ibrahim, kakan kakanninmu?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan