Saboda haka yanzu sai ku gyara al'amuranku da ayyukanku, ku yi biyayya kuma da muryar Ubangiji Allahnku. Ubangiji kuwa zai janye masifar da ya hurta gāba da ku.
Mai yiwuwa ne idan mutanen Yahuza suka ji dukan masifar da na yi niyya in aukar musu da ita, za su bar mugayen ayyukansu don in gafarta musu muguntarsu da zunubinsu.”
Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
Ku yi aikin da zai nuna tubanku, kada ma ku ko fara cewa a ranku Ibrahim ne ubanku. Ina dai gaya muku Allah yana da iko ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya daga duwatsun nan.
Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa'azi, sa'an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa'an nan kuma na yi wa al'ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.