Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 3:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Amma da Yahaya ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa, sun taho domin a yi musu baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 3:7
49 Iomraidhean Croise  

Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”


Wanda ba ya bin doka tare da mugaye yake, amma idan kana bin doka kai abokin gāban mugaye ne.


Kuna ƙyanƙyashe ƙwan kāsa, kuna saƙa da saƙar gizogizo. Duk wanda ya ci ƙwayayenku zai mutu, ƙwan da ya fashe zai ƙyanƙyashe kububuwa.


Ku gudu daga cikin Babila, Bari kowa ya ceci ransa, Kada a hallaka ku tare da ita, Gama a wannan lokaci Ubangiji zai sāka mata, Zai sāka mata bisa ga alhakinta.


Da wa zan yi magana don in faɗakar da shi, don su ji? Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, su ji, Ga shi, maganar Ubangiji kuwa ta zama abin ba'a a gare su, Ba su marmarinta.


Amma da Farisiyawa suka ji haka sai suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu kawai, wannan yake fitar da aljannu.”


Ku macizai! Yaya za ku iya yin maganar kirki, alhali kuwa ku mugaye ne? Don abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.


Sai almajiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisiyawa sun ji haushi da suka ji maganan nan?”


Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo suka roƙe shi ya nuna musu wata alama daga Sama, domin su gwada shi.


Sai Yesu ya ce musu, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”


Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa.


A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya,


Amma da Farisiyawa suka ji ya ƙure Sadukiyawa, suka taru.


Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta?


Ina dai gaya muku, in adalcinku bai fi na malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.”


Suka aiko masa da waɗansu Farisiyawa da mutanen Hirudus, don su burma shi cikin magana tasa.


Sai Sadukiyawa (su da suke cewa, wai ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka tambaye shi suka ce,


Ya gargaɗe su ya ce, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Hirudus.”


Farisiyawa kuwa da yake masu son kuɗi ne, da jin haka, suka yi masa tsaki.


Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu'a ga kansa ya ce, ‘Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan.


Amma Farisiyawa da masanan Attaura suka shure abin da Allah yake nufinsu da shi, da yake sun ƙi ya yi musu baftisma.


Su kuwa, Farisiyawa ne suka aiko su.


Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.


Da Farisiyawan nan da suke tare da shi suka ji haka, suka ce masa, “Wato mu ma makafi ne?”


Amma waɗansu masu ba da gaskiya, 'yan ɗariƙar Farisiyawa, suka miƙe, suka ce, “Wajibi ne a yi musu kaciya, a kuma umarce su, su bi Shari'ar Musa.”


Saboda haka sai ku zauna a faɗake, ku tuna, shekara uku ke nan ba dare ba rana, ban fasa yi wa kowa gargaɗi ba, har da hawaye.


Sun sani tun ainihi, in dai za su yarda su yi shaida, cewa lalle ni Bafarisiye ne bisa ga ɗariƙar nan da ta fi tsanani cikin addinin nan namu.


Amma babban firist ya taso, da duk waɗanda suke tare da shi, wato 'yan ɗariƙa Sadukiyawa, suna kishi gaya,


Gama ana bayyana fushin Allah daga Sama, a kan dukan rashin bin Allah, da aikin mugunta na mutanen da suke danne gaskiya, ta aikin muguntarsu,


To, tun da yake a yanzu an kuɓutar da mu ta wurin jininsa, ashe kuwa, ta wurinsa za mu fi samun kārewa daga fushin Allah ke nan.


ku kuma saurari komowar Ɗansa daga Sama, wanda ya tasa daga matattu, wato Yesu, mai kuɓutar da mu daga fushin nan mai zuwa.


Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya.


domin albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa sākewa, masu nuna, cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu ƙarfafa ƙwarai mu riski abin da muka kafa bege a kai.


Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan