Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 3:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk ƙasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurinsa,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 3:5
9 Iomraidhean Croise  

Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,


Taro masu yawan gaske suka bi shi daga ƙasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da ƙasar Yahudiya, har ma daga hayin Kogin Urdun.


Sai duk mutanen ƙasar Yahudiya, da dukan mutanen Urushalima suka yi ta zuwa wurinsa, suna bayyana zunabansu, yana yi musu baftisma a Kogin Urdun.


“Attaura da litattafan annabawa suna nan har ya zuwa ga Yahaya, daga lokacin nan kuwa ake yin bisharar Mulkin Allah, kowa kuma yana kutsawa zuwa ciki.


Sai ya zaga duk lardin bakin Kogin Urdun, yana wa'azi, cewa mutane su tuba a yi musu baftisma, domin a gafarta musu zunubansu,


Saboda haka, Yahaya ya ce wa taron jama'ar da yake zuwa domin ya yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?


Yahaya kuma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salima, domin da ruwa da yawa a can. Mutane kuwa suka yi ta zuwa ana yi musu baftisma.


Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan