Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 3:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Yahaya kuwa yana saye da tufa ta gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 3:4
12 Iomraidhean Croise  

Suka ce masa, “Ai, wani gargasa ne mai ɗamara ta fata.” Sarki ya ce, “Ai, Iliya ne Batishbe.”


A wannan lokaci Ubangiji ya riga ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz, cewa ya tuɓe tsummokin da yake saye da su, ya kuma tuɓe takalmansa. Shi kuwa ya yi biyayya ya yi ta yawo tsirara, ba kuma takalmi a ƙafarsa.


Za ku iya cin fara, da gyare, da ƙwanso da irinsu.


A wannan rana ce kowane annabi zai ji kunyar wahayinsa sa'ad da ya yi annabcin. Ba zai sa rigar gashi don ya ruɗi jama'a ba.


“Ga shi, zan aiko muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji ta zo.


“Ga shi, Yahaya ya zo, ya ƙi ciye-ciye da shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da iska.’


To, kallon me kuka fita? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon alharini a fada suke.


Yahaya kuwa na sanye da tufar gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.


Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya. Yă mai da hankalin iyaye a kan 'ya'yansu, Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai, Ya tanada wa Ubangiji jama'a, ya same su a shirye.”


“Ya sa shi ya hau kan tuddai, Ya ci amfanin ƙasa, Ya sa shi ya sha zuma daga dutse, Ya ba shi mai daga dutsen ƙanƙara.


Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi annabci kwana dubu da metan da sittin, suna a saye da tsummoki.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan