Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 3:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Wannan shi ne wanda Annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar mai kira a jeji yana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji tafarki, Ku miƙe hanyoyinsa.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa, “Ga murya mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 3:3
8 Iomraidhean Croise  

Murya tana kira tana cewa, “Ka shirya hanya a jeji domin Ubangiji! Ka share hanya a hamada domin Allahnmu!


A kan wannan ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya amsa, ya ce, “Zan aiki manzona don ya shirya mini hanya, sa'an nan Ubangiji wanda kuke nema zai zo farat ɗaya a cikin Haikalinsa. Manzon da kuke sa zuciyar zuwansa, yana zuwa, zai yi shelar alkawarina.”


Muryar mai kira a jeji tana cewa, Ku shirya wa Ubangiji tarfarki, Ku miƙe hanyoyinsa.”


Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya. Yă mai da hankalin iyaye a kan 'ya'yansu, Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai, Ya tanada wa Ubangiji jama'a, ya same su a shirye.”


Kai kuma, ɗan yarona, za a ce da kai annabin Maɗaukaki, Gama za ka riga Ubangiji gaba, Domin ka shisshirya hanyoyinsa,


Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan