idan sun koma cikin hankalinsu a ƙasar da aka kai su bauta, har suka tuba, suka roƙe ka a ƙasar, suna hurta zunubansu da irin muguntar da suka aikata, ka ji addu'arsu, ya Ubangiji.
Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’
A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.
A Ranar Shari'a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su kā da su, don sun tuba saboda wa'azin Yunusa. Ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.
Ya kuma ba su wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar yisti yake, wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗe da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”
“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga.
Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.
Ina dai gaya muku, haka kuma, za a yi farin ciki a Sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan adalai tasa'in da tara waɗanda ba su bukatar tuba.”
Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa ko wannenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki,
Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa'azi, sa'an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa'an nan kuma na yi wa al'ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.
Don baƙin ciki irin wanda Allah yake sawa, shi ne yake biyarwa zuwa ga tuba, da kuma samun ceto, ba ya kuma sa “da na sani”. Amma baƙin ciki a kan al'amarin duniya, yakan jawo mutuwa.
Saboda haka, sai mu ci gaba a kan ka'idodin farko na al'amarin Almasihu, har ya zuwa kammala, ba wai mu sāke koyar da jigajigan nan na tuba da ibada marar tasiri ba, da na gaskatawa da Allah,
Ubangiji ba ya jinkirta alkawarinsa, yadda waɗansu suka ɗauki ma'anar jinkiri, amma mai haƙuri ne a gare ku, ba ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba.
Ka tuna da komawa bayan da ka yi fa, ka tuba, ka yi irin aikin da ka yi tun daga farko. In ba haka ba, zan zo a gare ka in kawar da fitilarka daga wurin zamanta, sai ko in ka tuba.