Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 3:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Da aka yi wa Yesu baftisma, nan da nan da ya fito daga ruwan, sai ga sama ta dāre, ya ga Ruhun Allah na saukowa kamar kurciya, har ya sauka kansa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 3:16
14 Iomraidhean Croise  

Ikon Ubangiji zai ba shi hikima, Da sani, da gwaninta yadda zai mallaki mutanensa. Zai kuwa san nufin Ubangiji, ya kuma yi tsoronsa,


Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.


Ubangiji ya ce, “Amma ni, wannan shi ne alkawarina da su, Ruhuna da yake tare da ku, da kalmomina da na sa a bakunanku, ba za su rabu da bakunanku ba, ko daga bakunan 'ya'yanku, ko na jikokinku, tun daga wannan lokaci har abada.”


Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.


A ranar biyar ga watan huɗu, a shekara ta talatin, ina cikin waɗanda aka kai su bautar talala, muna kusa da kogin Kebar, sai aka buɗe mini sammai, na kuwa ga wahayi na ɗaukakar Allah.


Da fitowarsa daga ruwan sai ya ga sama ta dāre, Ruhu yana sauko masa kamar kurciya.


Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala'ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.”


Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba.


tun daga baftismar da Yahaya ya yi, har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi daga wurinmu aka kai shi zuwa Sama, wato ɗaya daga cikin mutanen nan ya zama shaidar tashinsa daga matattu, tare da mu.”


Sai ya ce, “Ga shi, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗan Mutum tsaye dama ga Allah.”


Shi ne wanda ya bayyana ta wurin ruwa da jini, Yesu Almasihu, ba fa ta wurin ruwa kaɗai ba, amma ta wurin ruwa da jini.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan