Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 3:11 - Littafi Mai Tsarki

11 “Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 “Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 3:11
29 Iomraidhean Croise  

Ta wurin ikonsa Ubangiji zai shara'anta al'ummar, ya kuma tsarkake ta, ya wanke laifin Urushalima, har da na jinin da aka zubar a can.


“Zan ba da ruwa ga ƙasa mai ƙishi, In kuma sa rafuffuka su yi gudu a hamada. Zan kwararo da albarka a kan 'ya'yanku, In sa albarkata kuma a kan zuriyarku.


Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta, Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa, Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya. Za su kira gare ni, Zan kuwa amsa musu, Zan ce, ‘Su jama'ata ne,’ Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”


yana yi musu baftisma a Kogin Urdun, suna bayyana zunubansu.


Yahaya Maibaftisma ya bayyana a jeji, yana wa'azi mutane su tuba a yi musu baftisma domin a gafarta musu zunubansu.


Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya. Yă mai da hankalin iyaye a kan 'ya'yansu, Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai, Ya tanada wa Ubangiji jama'a, ya same su a shirye.”


sai Yahaya ya amsa wa dukansu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake yi muku baftisma, amma wani yana zuwa wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in ɓalle ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.


Sai ya zaga duk lardin bakin Kogin Urdun, yana wa'azi, cewa mutane su tuba a yi musu baftisma, domin a gafarta musu zunubansu,


Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ”


Wannan shi ne wanda na ce, ‘Wani yana zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’


domin Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma kafin 'yan kwanaki da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.”


Bulus ya ce, “Ai, Yahaya baftisma ya yi a tuba, yana faɗa wa mutane su gaskata da mai zuwa bayansa, wato Yesu.”


Suna cikin tafiya, suka iso wani ruwa, sai bābān ya ce, “Ka ga ruwa! Me zai hana a yi mini baftisma?”


Sai ya yi umarni a tsai da keken dokin. Sai dukansu biyu suka gangara cikin ruwan, Filibus da bābān, ya yi masa baftisma.


Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda, mu zama jiki guda, Yahudawa ko al'ummai, bayi ko 'ya'ya, dukanmu kuwa an shayar da mu Ruhu guda.


Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,


sai ya cece mu, ba don wani aikin adalci da mu muka yi ba, a'a, sai dai domin jinƙan nan nasa, albarkacin wankan nan na sāke haihuwa, da kuma sabuntawar nan ta Ruhu Mai Tsarki,


Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan