Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 3:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Koyanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiya. Saboda haka duk bishiyar da bata bada 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 3:10
26 Iomraidhean Croise  

Amma wanda zai taɓa su, sai da wani ƙarfe ko da māshi, Za a ƙone su ƙurmus.”


Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama, Yakan ba da 'ya'ya a kan kari, Ganyayensa ba sa yin yaushi, Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.


Ka sa garwashin wuta yă zubo a kansu, Ka sa a jefa su a rami, kada su ƙara fita.


Adalai za su yi yabanya Kamar itatuwan giginya, Za su yi girma kamar itatuwan al'ul na Lebanon.


Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.


Domin in kawo wa masu makoki a Sihiyona Farin ciki da murna maimakon baƙin ciki, Waƙar yabo maimakon ɓacin rai. Ubangiji kansa zai lura da su, Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa. Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai, Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi.


Shi kamar itace ne wanda ake dasa a bakin rafi Wanda yake miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafin, Ba zai ji tsoron rani ba, Kullum ganyensa kore ne, Ba zai damu a lokacin fari ba, Ba zai ko fasa yin 'ya'ya ba.


Sai ya yi magana da ƙarfi, ya ce, “ ‘A sare itacen, a daddatse rassansa, A zage ganyayensa ƙaƙaf, a warwatsar da 'ya'yansa. A sa namomin jeji su gudu daga ƙarƙashinsa, Tsuntsaye kuma su tashi daga rassansa.


“Duba rana tana zuwa, sa'ad da dukan masu girmankai, da mugaye za su ƙone kamar tattaka, a ran nan za su ƙone ƙurmus ba abin da zai ragu, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Da ya ga wani ɓaure a gefen hanya, ya je wurin, amma bai sami kome ba, sai ganye kawai. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada ka ƙara yin 'ya'ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe.


Duk itacen da ba ya 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta.


In fa irin abubuwan nan suna faruwa ga ɗanye, yaya zai zama ga ƙeƙasasshe?”


Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin itatuwa. Saboda haka duk itacen da bai yi 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare shi, a jefa a wuta.”


Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa.


Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone.


Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?


Amma tsire-tsirenta ƙaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, tana kuma gab da la'antarwa, ƙarshenta dai ƙonewa ne.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan