Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 3:1 - Littafi Mai Tsarki

1 A wannan zamani ne Yahaya Maibaftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana wa’azi a Hamadan Yahudiya

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 3:1
27 Iomraidhean Croise  

Benaiya ɗan Yehoyada kuwa ya shiga alfarwar ya kashe shi. Aka binne shi a gidansa a karkara.


“Hakika ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya bayyana da ya fi Yahaya Maibaftisma girma. Duk da haka, wanda ya fi ƙanƙanta a Mulkin Sama ya fi shi.


Sun tafi ke nan, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa?


Sai suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa Iliya, waɗansu kuma Irmiya, ko kuwa ɗaya daga cikin annabawa.”


Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”


Ku yi aikin da zai nuna tubarku.


yana cewa, “Lokaci ya yi, Mulkin Allah ya kusato. Ku tuba, ku gaskata da bishara.”


Yadda yake a rubuce a littafin Annabi Ishaya cewa, “Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba, Wanda zai shirya maka hanya.


Kai kuma, ɗan yarona, za a ce da kai annabin Maɗaukaki, Gama za ka riga Ubangiji gaba, Domin ka shisshirya hanyoyinsa,


Baya jakadun Yahaya sun tafi, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa?


tun daga baftismar da Yahaya ya yi, har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi daga wurinmu aka kai shi zuwa Sama, wato ɗaya daga cikin mutanen nan ya zama shaidar tashinsa daga matattu, tare da mu.”


Ga shi kuwa, Ubangiji ya kiyaye ni har wa yau, kamar yadda ya faɗa, shekara arba'in da biyar ke nan, tun lokacin da Ubangiji ya faɗa wa Musa wannan magana, a lokacin da Isra'ilawa suke yawo a jeji. Ga shi yau ni mai shekara tamanin da biyar ne.


Zuriyar Bakene, surukin Musa kuwa suka fita tare da mutanen Yahuza daga birnin dabino, wato Yariko, suka tafi jejin Yahuda da take a Negeb kudu da Arad. A can suka zauna tare da Amalekawa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan