Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 28:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, domin wani mala'ikan Ubangiji ne ya sauko daga Sama, ya zo ya mirgine dutsen, ya zauna a kai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa. Don wani mala’ikan Ubangiji ya sauka daga sama, ya je kabarin, ya gungurar da dutsen, ya kuma zauna a kai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 28:2
12 Iomraidhean Croise  

ya sa shi a wani sabon kabari da ya tanadar wa kansa, wanda ya fafe a jikin dutse. Sai ya mirgina wani babban dutse a bakin kabarin, ya tafi.


Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka buga wa dutsen nan hatimi, suka kuma sa sojan tsaro.


To, a ranar farko ta mako, Maryamu Magadaliya ta je kabarin da asuba, tun da sauran duhu, ta ga an kawar da dutsen daga kabarin.


farat ɗaya, sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, har harsashin ginin kurkuku ya raurawa. Nan da nan ƙofofin suka bubbuɗe, marin kowa kuma ya ɓalle.


Amma da daddare sai wani mala'ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun, ya fito da su, ya ce,


Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, An bayyana shi da jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.


An dai bayyana musu, cewa ba kansu suke bauta wa ba, ku suke bauta wa, a game da abubuwan da masu yi muku bishara, ta ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda aka aiko daga sama suka samar da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala'iku suke ɗokin gani.


Sa'an nan aka buɗe Haikalin nan na Allah da yake a Sama, aka kuma ga akwatin alkawarinsa a Haikalinsa. Sai aka yi ta walƙiya da kururuwa, da aradu, da rawar ƙasa, da ƙanƙara manya manya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan