Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 28:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al'ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 28:19
39 Iomraidhean Croise  

Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.”


“Yanzu fa, sai ku matso kusa da ni, Ku ji abin da nake faɗa. Tun da farko na yi magana da ku a fili, A koyaushe nakan cika maganata.” (Yanzu Ubangiji Allah ya ba ni iko, ya kuwa aike ni.)


Ubangiji ya ce mini, “Bawana, ina da aiki mai girma dominka, Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba, Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai, Domin dukan duniya ta tsira.”


Ubangiji ya nuna ikonsa mai tsarki, Ya ceci jama'arsa, Dukan duniya kuwa ta gani.


Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida yake, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”


Za a tara dukan al'ummai a gabansa, zai kuma ware su dabam dabam, kamar yadda makiyayi yake ware tumaki da awaki.


har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi aka kai shi Sama, bayan ya yi umarni ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.


Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”


Bayan sun yi bishara a wannan gari, sun kuma sami masu bi da yawa, suka koma Listira da Ikoniya, da kuma Antakiya,


Waɗanda suka ya na'am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku.


To, sai ku sani, wannan ceto na Allah, an aiko da shi har ga al'ummai, su kam za su saurara.”


Nan take sai wani abu kamar ɓawo ya faɗo daga idanunsa, sai ya sāke gani. Sa'an nan ya tashi, aka yi masa baftisma.


Amma ina tambaya. Ba su ji jawabin ba ne? Hakika sun ji. “Muryarsu ta gama duniya duka, Maganarsu kuma ta kai har bangon duniya.”


In ba haka ba, mene ne nufin waɗanda ake yi wa baftisma saboda matattu? In ba a ta da matattu sam, don me ake yi wa waɗansu baftisma saboda su?


Alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su tabbata a gare ku duka.


Duk ɗaukacinku da aka yi wa baftisma ga bin Almasihu, kun ɗauki halin Almasihu ke nan.


Domin ta gare shi ne dukanmu biyu muka sami isa gun Uba ta hanyar Ruhu guda.


Sai dai fa ku nace wa bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata ƙaura daga begen nan na bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa dukkan talikan da suke a duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.


Baftisma kuwa, wadda ita ce kwatancin wannan, ta cece ku a yanzu, ba ta fitar da dauɗa daga jiki ba, sai dai ta wurin roƙon Allah da lamiri mai kyau, ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu,


Ruhu kuma shi ne mai ba da shaida, domin Ruhun shi ne gaskiya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan