Ka faɗa wa amintattun bayinka a wahayin da ka nuna musu tun da daɗewa, ka ce, “Na sa kambin sarauta a kan shahararren soja, Na ba da gadon sarauta ga wanda aka zaɓa daga cikin jama'a.
Kowane abu Ubana ne ya mallaka mini. Ba kuwa wanda ya san ko wane ne Ɗan sai dai Uban, ko kuma ya san ko wane ne Uban sai dai Ɗan, da kuma wanda Ɗan yake so ya bayyana wa.”
“Mai zuwa daga Sama yana Sama da kowa. Wanda yake na ƙasa asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma yake yi. Mai zuwan nan daga Sama yana Sama da kowa.
“Gama Allah ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa.” Amma da aka ce, “An sarayar da kome karƙashin ikonsa” a fili yake shi wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, a keɓe yake.
Kā sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa.” To, a wajen sarayar da dukkan abubuwa a ƙarƙashinsa ɗin nan, Allah bai bar kome a keɓe ba. Amma kuwa har a yanzu ba mu ga yana sarrafa dukkan abubuwa ba.
Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”
Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, Ɗan Ragon kuwa zai cinye su, shi da waɗanda suke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, amintattu, domin shi ne Ubangijin iyayengiji.”