Ku yi mubaya'a da Ɗan, Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu, Gama yakan yi fushi da sauri. Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!
Daga baya ya bayyana ga sha ɗayan nan, su kansu, sa'ad da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurinkansu, domin ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi ba.
Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuya tasa, tare da tabbatarwa masu yawa, masu ƙarfi kuma, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba'in, yana zancen al'amuran Mulkin Allah.