Sandunan akwatin dogaye ne ƙwarai, har ana ganin kawunansu a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki. Amma daga waje ba a iya ganinsu. Suna a wannan wuri har yau.
Joshuwa kuma ya kafa duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun, a wurin da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya, duwatsun suna nan har wa yau.