Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 27:64 - Littafi Mai Tsarki

64 Saboda haka sai ka yi umarni a tsare kabarin nan sosai har rana ta uku, kada almajiransa su sace shi, sa'an nan su ce wa mutane wai ya tashi daga matattu. Yaudarar ƙarshe za ta fi ta farkon muni ke nan.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

64 Saboda haka, ka ba da umarni, a tsare kabarin sai rana ta uku ɗin. In ba haka ba, almajiransa za su iya zuwa su sace jikin, sa’an nan su faɗa wa mutane cewa, an tashe shi daga matattu. Ruɗin ƙarshen nan fa, sai yă fi na farkon muni.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 27:64
5 Iomraidhean Croise  

Daga nan ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa. Haka zai zamar wa wannan mugun zamani.”


suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu.


Sai Bilatus ya ce musu, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare shi iyakar ƙoƙarinku.”


suka ce, “Ku faɗa wa mutane almajiransa ne suka zo da daddare suka sace shi kuna barci.


Ai, gargaɗin da muke yi muku babu bauɗewa ko munafunci a ciki, balle yaudara,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan